Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
An bayyana wakokin da a ke yi a yanzu a Masana’antar fina-finai ta Kannywood a matsayin jigo na tafiyar da harkokin masana’antar a yanzu, wanda ba don an koma yin wakokin ba, to da tuni babu wata sana’ar da a ke yi sai dai kowa ya kama gaban sa.
Fitaccen Darakta kuma Furodusa a masana’antar Aminu S Bono ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke tattaunawa da wakilin Jaridar Dimukaradiyya a kan yanayin da masana’antar ta ke ciki a yanzu.
Inda ya ke cewa “Maganar gaskiya a yanzu ba don an koma yin wakoki ba, to da tuni babu wani abin da a ke yi, saboda Mutuwar da kasuwar fim din ta yi, domin kuwa a yanzu kusan shekaru uku kenan babu wani sabon fim da ya shiga kasuwa saboda ana tunanin ko da an yi an kai kasuwa to kudin fa ba zai dawo ba, don haka ne sai duk jarumai suka koma yin waka, suna saka wa a YouTube ko shafukan su na Facebook,. ”
Ya ci gaba da cewar” Amma ko da aka koma yin wakokin ma, ba kudin da za a sayar da wakokin ba ne su ke kawo kudin, sai dai idan mutum ya yi wakar ko mace ko namiji to wannan ganin sa da a ke yi shi ne zai sa, ya samu masoya wadanda in harkar biki ta samu a gayyace shi, to ta haka ne a ke samun kudin, Amma ba don a yi wakar a sayar ba, don haka dai a yanzu zan iya cewa, da kai harkar fim duk yan dabaru ne, kawai a wannan lokaci. ”
A karshe ya yi kira ga mutane masu gudanar da harkokin a masana’antar da su yi kokarin rike mutuncin su da kimar su ta yadda za a rinka yi wa sana’ar kollon mutunci, kamar yadda sauran harkokin sana’a su ke.