Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sanar da sallamar mai horas da ƙungiyar Quique Setién.
Sanarwar da Barcelona ta fitar a yau Litinin 17 ga watan Agusta ta ce, sallamar kocin na daga cikin garambawul ɗin da zata yi domin kawo sabon yanayi a ƙungiyar.
“Daga yanzu Quique Setién ba shi ba ne kocin ƙungiyar mafi tashe. Nan gaba za a sanar da sabon kocin, daga cikin sauye-sauyen da muke yi”, kamar yadda ƙungiyar ta wallafa a shafinta na twitter.
Ta ce kwamitn amiintattun ƙungiyar ne suka amince da shawarar sallamar Quique Setién, wanda ya fara horas da ‘yan wasanta a ranar 13 ga Janairu, 2020.
A tsawon zamansa na wata bakwai, Quique ya jagoranci kungiyar a wasanni 25.
A cikinsu wasannnin ya samu nasara a 16, ya yi kunnen doki 4 sannan yayi rashin nasara 5.
Wannan mataki da ƙungiyar ta ɗauka na da nasaba da irin rashin nasara da kocin yayi musamman wajen gaza ɗaukar gasar Laliga wanda ƙungiyar Real Madrid ta lashe, sannan da rashin nasara da ƙungiyar ta yi a gasar Super cup, sannan uwa da rashin nasarar da ta yi a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich da ci 8-2 a gasar nahiyar zakarun Turai.