Ƴan bindiga sun kai hari ga Jami’an Hukumar FRSC ta Anambra, sun Kashe Mutum 2
Wasu ƴan bindiga sun kai hari ga wani wuri na Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa ta Jahar Anambra, tare da kashe jami’ai biyu da raunata wasu.
Tawagar Jami’an sun kasance suna gudanar da sintiri akan hanyar Igbo-Uku da misalin ƙarfe 2.45 a ranar Lahadi, a lokacin da ƴan bindiga suka buɗe wa Direba da Jami’ai guda biyu, inda na huɗun ya tsere cikin daji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar APC Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ondo
Mai Kula da Ilmi na Hukumar Bisi Kazeem ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa mai taken “Jami’ai guda biyu an harbe su a yayinda ƴan bindiga suka kai hari ga Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa a Jahar Anambra.
Sanarwar tace Shugaban Tawagar da ya samu raunuka, an yi saurin kaishi Asibiti domin yi mashi magani.
Sanarwar ta ƙara dacewa “Shugaban Hukumar na Ƙasa Dr Boboye Oyeyemi wanda ya kaɗu da lamarin ya koka kan harin, yana mai ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, Shugaban Tawagar, da Jami’an Hukumar, da dukkanin Shuwagabancin Hukumar da Ma’aikata, sai yayi addu’a Allah yajiƙan su.”
Oyeyemi yasha alwashin cewa Hukumar na aiki da Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa da sauran Hukumomin tsaro domin tabbatar dacewa waɗanda suka kai harin an kamo su.