By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya koma jam’iyyar Labour Party.
Obi ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a yayin da ya yi rajista da jam’iyyar a gundumarsa ta Agulu dake jihar Anambra.
Da yake bayar da dalilan shiga jam’iyyar Labour, Obi ya ce: “Tunda na fice daga PDP saboda al’amuran da suka ci karo da mutuntaka da ka’idata, na tuntubi bangarori daban-daban da kuma wasu mutane domin ganin ba mu kawo cikas ga hanyar da za mu bi wacce ba ta dace da wurin da ake so ba.
“A gare ni, tsarin cimma burinmu yana da mahimmanci kamar abin da mutum zai yi bayan haka.
“Saboda haka, na zabi hanyar da nake ganin ta dace da burinmu na daga cigaban kasar nan.
“kuma ita ce jam’iyyar Labour wadda ta yi daidai da jama’a, ma’aikata, ci gaba, samarwa, tabbatarwa da kuma hada kan ‘yan Najeriya a matsayin iyali daya.
“Ina gayyatar duk ‘yan Najeriya da su zo tare da ni wajen kwato kasarmu.
“Ka tabbata cewa ba zan taɓa barin ka ba.”
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 25 ga watan Mayu Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ya bayyana janyewar sa daga neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP da kuma ficewa daga cikin ta kasa da sa’oi 72 kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa Obi wanda ya marawa Atiku Abubakar baya a zaben shekarar 2019 ya rubuta wasikar ficewar sa daga Jam’iyyar ne ga shugaban ta Iyorchia Ayu ba tare da gabatar da dalilan daukar wannan mataki ba.
Wasikar ta bayyana cewar Obi ya gabatar da aniyar sa ta janyewa daga PDP kamar yadda doka ta tanada inda ya shaidawa shugaban mazabar sa dake Agulu ta 2 a Anaocha ta Jihar Anambra daga ranar 20 ga watan Mayu, matakin da ya kawo karshen aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar.
Tsohon gwamnan wanda ya bayyana aniyar sa ta bada gudumawa wajen gina kasa, yace halin da ake ciki yanzu ba zai bashi damar yin haka ba ta hanyar da ta dace, duk da yake babu abinda ya sauya a shirin sa na bada gudumawa wajen ceto Najeriya.
Sai dai Daraktan yakin neman zaben sa Doyin Okupe ya tabbatar da cewar Obi zai tsaya takaran zabe mai zuwa ba tare da bayyana jam’iyyar da zai koma ba.