Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama, Abba Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda hudu bisa zarginsu da hannu a wata badakalar hada baki wajan saffarar miyagun kwayoyi.
Sauran laifuffukan da aka lissafa a kansu sune, rashin da’a, cin hanci da rashawa a hukumance da dai sauran su.
Kamen jami’an ya biyo bayan bayanan Wani Faifan Bidiyon da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce ta samu a ranar 10 ga watan Fabrairun 2022.
Mai magana da yawun rundunar Yan sanda ta kasa, Muyiwa Adejobi,ya tabbatar da Kama Abba Kyari a wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Litinin.