A yau juma’a Sefero Janar na yan sandan kasar nan, IGP Usman Baba ya bada Umarnin tura sabbin kwamishinonin yan sanda 13, a shelkwatocin rundunar dake fadin kasa nan, har da Babban birnin tarayya Abuja.
Usman Baba ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Mai magana da yawun rundunar ta kasa Frank Mba, inda ya ce,tura sabbin kwamishinonin an yi shi ne domin samun dai-dai-to, bisa a harkar tsaron cikin gida a fadin kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NiMET ta yi Hasashen samun ruwan sama kamar da bakin kwarya
Jihohin da suka Sami sabbin Kwamishinonin sun hada da: jihar Niger Wanda CP Monday Bala Kuryas zai kama Aiko, jihar Kwara CP Emienbo Tuesday Assayamo, jihar Nasarawa CP Soyemi Musbau Adesina, jihar Taraba CP Abimbola Shokoya, jihar Benue CP Akingbola Olatunji, Babban birnin tarayya Abuja CP Babaji Sunday, jihar Kogi CP Arungwa Nwazue Udo.
Sauran sun hada da: jihar Kaduna CP Abdullahi Mudashiru, jihar Jigawa CP Aliyu Sale Tafida, jihar Enugu CP Abubakar Lawal, jihar Cross River CP Alhassan Aminu, jihar Bayelsa CP Echeng Eworo Echeng sai Kuma jihar Kebbi CP Musa Baba.
Kazalika Usman Baba ya yi kira ga sabbin kwamishinonin da su amshi aikin jagorancin Shalkwatar su a nan take, san nan Kuma su dauki dammarar yaki da dukkannin nau’in ta’adanci a yankunan su.
Awani labarin Kuma..
Kutu ta tsare wani Mutum, da yayi wa wata Mai tabin hankali fyade a Kano
A yau juma’a ce wata Kotun Majistiri dake zaman ta a garin Kano, ta bada umarnin cigaba da tsare wani mutum mai suna Mohammed Sani a gidan gyaran hali, bisa zargin yi wa wata budurwa mai fama da tabin hankali Fyade.
Rahotanni sun nuna cewar, budurwar na da shekara 15 me Kuma na fama da lalurar tabin hankali.
Rundunar yan sandar jihar ce ke jagorantar tuhumar Sani Mai shekara 46, dake zaune a Rijiyar Zaki dake cikin garin Kano, kan zargin sa da yiwa budurwar fyade, Wanda ya saba wa sashin doka na 283 na kundun dokar Penal Code.
Kazalika kafin yanke hukuncin Mai gabatar da kara Asma’u Ado ta bayyana wa Kotun cewa, Wanda ake zargin, ya aikata wannan aika-aikan ne a ranar 11 ga watan Yulin Shekarar nan, a yankin Rijiyar Zaki da ke birnin Kano.
Ta kara da cewa, da musalin karfe 11 na safe ne, wanda ake zargin ya kai yarinyar mai fama tabin hankali dakin shi, inda ya yi mata fyade.
Anashi bangaren Mohammed Sani ya karyata zargin da ake yi ma shi, a gaban Kotun.
Sai dai Mai shari’an Kotun na Majistiri Mustapha Sa’ad-Datti, ya dage sauraran karar harzuwa ranar 28 ga watan Ogustan shekaran nan, domin cigaba da sauraran karar.