Rahotanni dake zuwa ga Jaridar Dimokuraɗiyya na nuni dacewar, a halin yanzu an buɗe layukan sadarwa a Sauran Ƙananan Hukumomi 7 na Jahar Katsina.
Sai dai mazauna garin sun shaida cewa, a halin yanzu layin MTN kaɗai ne ya fara dawo wa, inda suke saran cewa, nan da wani lokaci sauran layukan zasu dawo.
KARANTA WANNAN LABARIN: A Cikin Harkar Fim Na Hadu Da Mutanen Kirki Da Na Banza – Nadiya Adamu
A wani rubutu da wani Mazaunin garin Ƙankara ya wallafa a shafin sa na Facebook mai suna Comr Nuhu Umar ya bayyana cewar ” Masha Allah layukan sadarwar mu sun dawo, Allah ya bamu zaman lafiya a yankin mu dama Ƙasa baki ɗaya.”
Haka zalika a lokacin da, Wakilin Jaridar Dimokuraɗiyya ya tuntuɓi wani Mazaunin gari Jibia Umar Sha’abu ya shaida cewa, tuni sun fara gaisawa da ƴan uwan su, dake wajen Jahar, wanda suka daina sakamakon rashin network.
Sai dai a sa’ilin da muka so jin tabakin wani Mazaunin Batsari da yake da zama a Katsina Mubarak Mohammed, ya bayyana cewar, har yanzu layukan sadarwar su bai dawo ba, amma suna saran zai dawo.
Amma a dukkanin ƙananan hukumomin a halin yanzu network nasu ya dawo.
Wannan na zuwa ne, bayan sanya doka da Gwamnatin Jahar Katsina tayi, inda ta bada umarnin kulle layukan domin magance ayyukan ƴan ta’adda a Jahar, inda daga bisani aka maido da layukan sadarwar, amma aka bar ƙananan hukumomi 7.