By Ishaq Dabai
Taron, wanda aka hana ‘yan jarida halarta, yana gudana ne a sabon katafaren ginin zamani da aka kaddamar a gidan gwamnatin Imo dake Owerri.
Wadanda suka kasance a taron sun hada da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, da mataimakin Gwamnan jihar Abia Ude Okechukwu.
Sauran sun hada da shugaban kungiyar Ibo ta duniya ta Ohanaeze Ndigbo Worldwide, Farfesa George Obiozor; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; Ministan jiha, Cif Uche Ogar: da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Tuni shugaba Buhari ya kaddamar da aikin titin Ihiagwa zuwa Nekede, da kuma ‘Balloon technology-driven underground tunnel’ da hanyar ruwa a titin Chukwuma Nwoha, da titin Naze/ Nekede/Ihiagwa, da sauran su.