An kashe wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a Owerri, babban birnin jihar Imo.
Lamarin ya faru ne kasa da awanni 48, bayan an kona ofishin hukumar a Nnewi na jihar Anambra.
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa, an harbe jami’in, mai suna Prince Nwachinaemere Ezemuonye Ozuzu, dan asalin unguwar Umuoyo, na garin Irete a karamar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo, an harbe shi har lahira ne a hanyar Owerri Onitsha.
Rahotanni sun nuna cewa, hukumar ta tura jami’in ne don aiki a Anambra ‘yan sa’o’i kadan bayan kona ofishin DSS a Nnewi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudin 2022 ranar Alhamis
Kazalika jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an kashe jami’in na DSS ne yayin da yake komawa Ofishin hukumar sa.
Haryanzu ba’a Sami cikakkun bayanai kan mutuwar jami’in ba, Amma An ce harsashin da wani abokin aikinsa ya harba bisa kuskure ne ya same shi.
Daya daga cikin ‘yan uwan nasa, Deacon Daniel Opara, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana abin a matsayin abin takaici.
Ya Kara da cewa, “Ya shiga aikin ne kimanin shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata, kuma ya yi aure da yara hudu.”
A nashi bangaren, Harkawo hada wannan rahoton, Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar CSP Mike Abattam, ba a iya samun sa ta wayar tarho ba, yayin da wayar sa ta kammala kara.
Comments 1