An kama wani Ba’amurke dauke da makamai a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) dake jihar Legas.
Fasinjan namiji (da aka sakaya sunansa) ya iso kasar nan ne a cikin jirgin United Airlines daga birnin Houston na kasar Amurka, wanda ya sauka da karfe 10:10 na safe.
An ce fasinjan ya shigo da bindigu ba tare da Ka’ida ba kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada kan jigilar bindigogi.
An gano bindigogin da suka hada da bindigar hannu, da kuma kirar Barretta da harsashi 26 na 9mm a cikin jakkunan mutumin.
An kuma ce fasinjan yana dauke da fasfo din kasa da kasa guda biyu; Najeriya da kuma na kasar Amurka.
Wata majiya ta filin jirgin ta shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa Ba’amurken bai bayyana makaman asari ba yayin da suka iso a filin jirgin ba.
Wata majiya ta shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa fasinjan yana da wasu takardu daga kasar Amurka, wadanda suka ba shi damar daukar bindigogi, amma ba a iya tantance sahihancin takardun ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana ci gaba da yiwa fasinjan tambayoyi a ofishin kula da shige da fice da ke filin jirgin na Legas.