Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama shahararren mawakin nan na Najeriya, Ice Prince, bisa laifin cin zarafin wani jami’in dan sanda.
An tattaro cewa da misalin karfe 3 na safiyar ranar Juma’a ne jami’an ‘yan sanda suka kama fitaccen mawakin nan Oleku crooer bisa laifin tuki ba tare da lacicin mota ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kimanin Naira Biliyan 11.9 Aka Wawure Cikin Shekaru Takwas A Jihar Kwara – Rahoto
Ice Prince wanda da farko ya amince a kai shi ofishin ba tare da bata lokaci ba, ya yi awon gaba da dan sandan a cikin motarsa, ya afka masa, sannan ya yi barazanar jefa shi a cikin tafkin.
Da yake tabbatar da kamun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an kama Ice Prince kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya a yau.
A cewar Hundeyin “Da misalin karfe 3 na safe @Iceprincezamani an dakatar da shi ne saboda tukin mota ba tare da lasisi ba Ya amince a kai shi ofishin ‘yan sanda.”
“Daga nan ne ya yi awon gaba da dan sandan da ke cikin motarsa, ya afka masa, sannan ya yi barazanar jefa shi a cikin kogin. An kama shi kuma yau za a gurfanar da shi a gaban kuliya.”
A wani labarin kuma, ASUU: Jami’ar Jihar Gombe Ta Janye Yajin Aiki, Ta Bude Rijista ga Malamai
Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a ranar Alhamis ta umurci dukkanin Ma’aikatan Makarantar da su koma bakin aiki cikin gaggawa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta cikin gida mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Dr Abubakar Aliyu Bafeto.