Kimanin mutane biyar ne ake fargabar sun mutu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a rumfunan zabe biyu a yayin zaben kananan hukumomi a jihar Enugu, ranar Laraba.
Yan bindigar sun mamaye rumfunan zabe da ke Obeagu ward III a karamar hukumar Enugu ta Kudu da kuma wata rumfar zabe da ke Akpugo a karamar hukumar Nkanu ta Yamma.
Masu dauke da makamai sun tarwatsa dandazon Jama’a ne ta hanyar lalata kayayyakin zabe bayan sun fatattaki masu kada kuri’a.
Baya ga wadanda aka kashe, wasu sun samu raunuka yayin da aka kona motoci da dama.
Wani ganau da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce an ji ’yan bindigar suna kururuwa cewa sun yi gargadin cewa kada a sake yin zabe a wani yanki na Kudu maso Gabas.
Da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sanda a Enugu, Daniel Ndukwe, ya shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa ya sake kiransa saboda yana cikin aiki.