An rantsar da tsohon kwamishinan shari’a kuma babban lauya a jihar Oyo Barista Abdulroheem Adebayo Lawal a matsayin sabon mataimakin gwamna a jihar Oyo.
Lawal wanda dan asalin yankin Oke Ogun ne ya yi rantsuwar ne a karkashin jagorancin babban alkalin jihar, Mai shari’a Munta Abimbola.
An gudanar da bikin ne a garin Ibadan a yau Litinin.
Lawal, har zuwa lokacin da aka nada shi, shi ne shugaban hukumar gidaje ta jihar Oyo.
Jaridar DAILY POST ta rahowaito cewa Lawal ya maye gurbin Injiniya Rauf Olaniyan.
Idan ba’a manta ba, Yan majalisar dokokin jihar Oyo da ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun tsige Olaniyan wanda dan kabilar Igboho ne kuma a shiyyar Oke Ogun a yau Litinin.
‘Yan majalisar a zamansu sun kuma amince da sunan Bayo Lawal a matsayin wanda zai maye gurbin Olaniyan.
A baya dai Jaridar Dimokiradiyya ta ruwaito cewa tsige Olaniyan na zuwa ne makonni kadan bayan ya fice daga PDP ya koma APC.
Gwamnan jihar wanda ya halarci bikin rantsarwar, ya bayyana nadin sabon mataimakin gwamnan a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyansa na isar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar jihar.
Makinde ya hori Lawal da ya saka maslahar jihar a gaba da yiwa jihar hidima da himma a sabon mukaminsa nasa.
A wnai labarin kuma na daban.
Wani Matashi Ya Afka Rijiya A Jihar Kwara
Wani matashi dan shekara 25 mai suna Banji Adebayo ya rasa ransa a ranar Litinin bayan da ya fada cikin rijiyar gida a jihar Kwara.
Lamarin ya faru ne a yankin Ile-Nla na garin Omu-Aran, dake karamar hukumar Irepodun ta jihar.
An ruwaito cewa wanda abin ya shafa, wanda ya je diban ruwa ne, ya tsunduma cikin rijiyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya ce an tsinto gawar wanda aka mutumin tare da mikata ga iyalansa.
Ya ce, “Daraktan ma’aikatar, Prince Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su yi taka tsantsan a harkokinsu na yau da kullum.”