An samu rudani a ranar Alhamis yayin da wasu mutane suka gano wata na’ura da ake zargin bam ne a Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Tashar jirgin kasa ta Kaduna tana unguwar Rigasa ne a jihar ta Kaduna.
Lamarin ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai kan wani jirgin kasa dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren ranar Litinin, inda fasinjoji akalla mutum takwas suka mutu, yayin da 26 suka samu raunuka, wasu kuma ba a tantance adadinsu ba aka yi garkuwa da su.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilin Jaridar PUNCH cewa an gano bam din ne a cikin bokitin da ke kan hanyar Makarfi a cikin al’umma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an rundunar sun yi nasarar kwance bam din.
Jalige ya ce an tura jami’an rundunar dake kwance bama-bamai zuwa wurin bayan da aka samu labarin.
Kakakin ‘yan sandan ya bukaci mazauna yankin da su kai rahoton duk wani motsi da suka samu, ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.