Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki Jagoran gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho.
Gamayyar Kungiyoyin Yarabawa, Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran ta gwamnatin Jamhuriyar Benin’.
Sai dai Babu Cikakkun bayanai game da sakin nasa har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta sake mai fafutukar kare hakkin kabilar Yarabawa, Cif Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho.
“An saki mai fafutukar ne a ranar Litinin ga Shugaban Yarbawa kuma Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Yarabawa ta, Ilana Omo Oodua ta Duniya, Farfesa Banji Akintoye da kwararre a Harshen Faransanci/Mataimakin Alana na Omo Oodua , Farfesa Wale Adeniran sun tabbatar da sakin nasa”.
“Akintoye ya bayyana sakin Ighoho a matsayin nasarar gaskiya akan duhu a kasar Yarbawa.”
Igboho, wanda ya tsallake rijiya da baya daga wani hari da jami’an tsaro suka kai masa a gidansa da ke Ibadan a ranar 1 ga Yuli shekarar 2021, an kama shi ne a Jamhuriyar Benin a kan hanyarsa ta zuwa Jamus a ranar 19 ga watan Yulin bara, tare da matarsa Mai suna Ropo.