Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa ya soke tarukan da za a yi na Babbar Sallah a jihar baki daya, tare da dakatar da dukkanin Sarakunan jihar guda biyar masu daraja ta daya daga gudanar da hawa a lokacin sallar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ‘yan jarida a garin Dutse babban birnin jihar, inda ya ce an soke tarukan ne a wani mataki na ci gaba da yaki da korona, inda ya ce jihar na yin nasara a wajen yaki da korona a cikin kwana 30 da ya gabata, inda a tsawon wannan kwanakin ba a samu masu cutar ba.
A cewar gwamnan cikin motoci 150 na abinci da za a kawo jihar domin bayar da tallafi ga marasa galihu, ya zuwa yanzu motoci 150 sun iso jihar.
Ya tabbatar da cewa za a raba kayayyakin abincin ne a gundumomi 287 dake kananan hukumomi 27 na jihar. Gwamnan ya tabbatar da cewa mutum daya kawai ya rage a cibiyar killace jama’a na jihar. A yayin da cibiyoyin killace jama’a dake Fanisau da Birninkudu an rufe su, sai dai ana ci gaba da cibiyoyin domin zaman shirin ko ta kwana.