An gano yaran biyu masu shekaru hudu, Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim da aka sace a unguwar Ijesha da ke Legas.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tsinci yaran da ransu a cikin wata karamar motar bas da aka yi watsi da ita tare da yaran a kan hanyar Oshodi zuwa Apapa Expressay da safiyar yau.
Mahaifiyar Dauda, Awau, ta shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa a halin yanzu an Kai yaran asibiti domin duba lafiyar su.
“Mun same su. An same su a cikin wata karamar motar bas da aka yi watsi da ita a safiyar yau a kan babbar hanyar. Suna kwance a asibiti yanzu,” in ji mahaifiyar.
Rahotanni sun nuna cewa kananan yaran sun bace ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma’a, sa’o’i biyu bayan dawowarsu daga makaranta.
An ce wani mutum ne ya yaudare su a babur mai kafa uku da biskit a lokacin da suke wasa a kusa da gidan su, sannan ya tafi da su.