Wani fashewa abu mai kama da Bom ya afku a cocin St Francis Catholic da ke titin Owa-luwa a garin Owo, karamar hukumar Owo a jihar Ondo.
Lamarin dai ya faru ne a yau Lahadi, kuma yanzu haka ana fargabar fashewar ta hallaka wasu masu ibada sakamakon lamarin.
Fashewar, rahotanni sun ce ta afku ne a harabar cocin a lokacin da jama’a ke ci gaba da gudanar da taron ibadar.
Wata majiya ta ce lamarin ya haifar da barkewar zullumi a zukatan mazauna yankin yayin da mazauna unguwar da ke cikin cocin suka gudu domin tsira da rayukansu.
Kawo wannan lokaci dai rundunar Yan Sandan jihar ba ta ce Komai dangane da wannan lamari.
Wata majiya kuma ta ce wasu makiyaya ne da ake zargin sun kai hari coci tare da kashe masu ibada.
Allah kabamu zaman lafiya a kasar mu dama duniya gaba daya amin.