Tsohon ɗan wasan tsakiya na Super Eagles, Emmanuel Ebiede, ya mutu a ranar Juma’a a birnin Port Harcourt, na jihar bayan ya yi fama da matsalar kumburin hanta.
Ebiede, mai shekara 47, a duniya mutu ne da misalin ƙarfe 4 na yamma a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Rivers. Jaridar The Punch ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Majalisar Zamfara Ta Tsawaita Wa’adin Shugabannin Kananan Hukumomi
Ya mutu ya bar matar aure ɗaya da ƴaƴa uku, biyu na rayuwa a Najeriya ɗaya yana rayuwa a ƙasar Holland.
Ɗan wasan tsakiya yana cikin ƴan tawagar Flying Eagles a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika na matasa wanda aka buga a Najeriya a shekarar 1995.
David Doherty, wanda yayi takarar neman shugabancin hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya (NFF), shine ya tabbatarwa da majiyar mu mutuwar ɗan wasan na kulob ɗin SC Heerenveen.
“Ina cikin baƙin ciki yanzu haka da muke magana. Duka kwana biyu muka yi magana da shi domin sanin halin da jikin sa yake.” A cewar sa
Ebiede sau biyu ya taɓa takawa Super Eagles leda.