Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal ta sallami masu horas sa yan wasan ta biyu daga ciki har da mai shekara 30 yana kungiyar.
Steve Bould wanda shine mai horas da yan wasan kungiyar yan kasa da shekara 23, ya shafe shekara 30 a Ƙungiyar a matsayin dan wasa da kuma mai Horaswa.
Kazalika Ƙungiyar ta sallami tsohon Kocin PSG Bruno Mazzioti bayan shafe kasa da shekara guda a Ƙungiyar yana kula da lafiyar yan wasa.
Wannan ka iya zama wani mataki na tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, domin akwai dambarwa kala-kala da ma a Ƙungiyar.
Korar Masu horaswan ba ta rasa nasaba da halin tasko da kungiyar ta shiga a kakar bana ganin cewa ta karkare gasar ne a wani mummunar mataki wanda ba ta taɓa fadawa ba a tarihin ta na Firimiya
Bould ya lashe gaser Firimiya uku da kuma FA biyu sa’ilin yana taka leda wa Ƙungiyar inda ya buga mata wasanni 287.