Kungiyar malaman jami’o’i ta sha alwashin daukaka kara kan umarnin kotun kula da da’ai Ma’aikata ta kasa, inda ta umurci malaman da su koma bakin aikin au cikin gaggawa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kungiyar ta ce ta fara hada lauyoyinta karkashin jagorancin fitaccen dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, babban lauyan Najeriya, domin shigar da kara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Kubutar Da Wani Mutum Daga Hannun Yan bindiga, Sun Kwato Harsasai
Shugaban kungiyar na shiyyar Legas, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar ya bukaci mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu tare da hada kai don kai wa ga fafutukar har zuwa karshe.
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa ASUU ta fara yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu domin amsa bukatunta da suka hada da amincewa da tsarin biyan albashi da kungiyar ta fi so ayi amfani da shi a maimakon IPPIS naa Gwamnatin Tarayya.
AWANI LABARIN KUMA: Shugaban Senegal Ya Nemawa Kasashen Afrika Alfarma A Taron MDD
Da yake jawabin a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 a birnin New York, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi kira da a dage takunkumin da aka kakabawa Zimbabwe.
Shugaban kasar Senegal, kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka na yanzu, ya ce matakan da ake dauka kan kasar Zimbabwe na kara ta’azzara al’ummar kasar cikin kangin talauci.