Wasu ‘yan bindiga sun kai samame a wasu gidaje dake Anguwar Maji, cikin garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen 22 bayan sa’o’i 24 da ziyartar babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba.
Jere, wanda ke da iyaka da Tafa-Sabon-Wuse a Jihar Neja, na kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Wani mazaunin Anguwar Maji, Shehu Bala, wanda ya tabbatar da sace mutanen na baya-bayan nan ta hanyar tattaunawa da wakilin Jaridar Daily Truat ta wayar tarho a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi.
Ya ce ‘yan bindigar wadanda suka zo da yawa dauke da bindigu kirar AK-47, sun mamaye wasu gidaje inda suka yi awon gaba da mutane 22 ciki har da mata biyar.
“’Yan bindigar sun zo da adadi mai yawa yayin da wasunsu ke sanye da kakin sojoji.
“Sun shiga gida gida suna tada wadanda abin ya shafa kafin su shiga daji da su,” in ji shi.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun shafe sama da awa daya suna gudanar da ayyukansu cikin natsuwa a cikin Garin na Jere..
Ya kara da cewa sun fara harbe-harbe ne kawai don tsoratar da mutane daga bin su bayan sun bar yankin.
Bala ya ce daya daga cikin mutane 22 da aka yi garkuwa da su ya tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi yayin da ake kai su cikin daji.
Sai dai harkawo hada wannan rahoto Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalinge, an kasa samunsa ta wayar tarho domin tabbatar da sace mutanen na baya-bayan nan.