Wasu bama -bamai a gefen hanya sun tashi kusa da wata motar safa da ke dauke da sojoji, a babban birnin kasar Siriya da sanyin safiyar yau Laraba, inda mutane 14 suka mutu wasu kuma suka samu raunuka, in ji gidan talabijin na kasar.
Harin shi ne mafi muni a Damascus cikin shekaru masu yawa, kuma abin da ba a saba gani ba tun lokacin da dakarun gwamnati suka kwace yankunan da ‘yan tawaye ke rike da su a cikin rikicin shekaru goma na Siriya.
Tashar talabijin ta Syria ta nuna hoton motar bas da ta kone a tsakiyar birnin Damascus, inda ta ce fashewar ta auku ne yayin da mutane ke kan hanyarsu ta zuwa aiki da makaranta.
Kazalika Rahoton ya ce, an gano bam na uku kuma an magance shi, kafin ya tarwatse a wannan yanki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Gargajiya na Niger ya shaki iskar Yanci, bayan Kwashe kwanaki 45
Sai dai har kawo hada wannan rahoto Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, Wanda aka kai a inda motoci ke haduwa da fita zuwa unguwanni daban -daban na babban birnin.
Kwamandan ‘yan sandan yankin Damascus Manjo Janar Hussein Jumaa ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa, “Wannan aikin matsoraci ne, ya kara da cewa, rundunar’ yan sanda ta killace yankin nan take, kuma ta tabbatar babu sauran bama -bamai” a cewar shi
Ya bukaci mutane da su sanar da hukumomi game da duk wani abu da ake ake dar-dar da suka gani a fadin yankin.
Jumaa ya ce daya daga cikin wadanda suka samu raunuka ya mutu sakamakon raunin da ya samu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 14.