Sarkin Bungudu na jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru ya sake shakar iskar yanci bayan ya kwashe kwanaki 30 a tsare a hannun Yan bindiga.
Wata majiya a fadar sarkin da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar wa Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, a daren jiya Alhamis wadanda suka yi garkuwa da shi suka saki sarkin.
Idan za a iya tunawa an yi garkuwa da Sarkin ne a ranar 14 ga watan Satumba, shekarar 2021, lokacin dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ‘yan bindiga suka yi wa motar sa kwanton bauna, Wanda ya haifar da musayar harbe -harbe tsakanin Yan bindigan da Hadiman Sarkin, Wanda yayi sanadiyar, an kashe wani jami’in dan sanda.
A majiyar “Sarkin zai nemi kulawar likita kafin ya wuce Zamfara. Muna jira mu tarbe shi. ”
KARANTA WANNAN LABARIN: Ni bance an bani kyautar Mota a Dubai ba, inji Daso
Idan za’a iya tunawa cewa, an biya Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa don sakin sarkin da ke cikin rudani, amma daga baya wadanda suka yi garkuwa da shi sun canza tunanin su, kuma suka ki sakin sa a maimakon haka sun sake yin wata sabuwar bukata ta Naira miliyan 100.
Don haka, ba a bayyana ko an biya Naira miliyan 100 bane, ko ba a biya ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ko gwamnatin jihar Zamfara ba ta fitar da wata sanarwa ba, kan sakin Basaraken