Yanzu-Yanzu: Buhari na ganawa da Shugaban APC, Gwamnoni, gabanin Zaɓen Fidda Gwani
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a daren Lahadi yana ganawa da wasu manyan Jiga-Jigan APC zuwa liyafar cin Abinci a ɗakin taro na Villa, Abuja.
Manyan Jiga-Jigan Jam’iyyar APC sun haɗa da Shugaban Jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu, da tsohon Sakataren Jam’iyyar Bisi Akande, da John Oyegun, da Sakataren Jam’iyyar Sanata Iyiola Omisore, da wasu Gwamnonin APC.
.KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnonin Arewa sun murƙushe damar Atiku na zama Shugaban Ƙasa — Cewar DG VON
Taron na daga cikin cigaba da tattaunawa da Shugaban Ƙasa ke yi da masu ruwa da tsaki da dama, domin zaɓar Dan Takarar Shugaban Ƙasa ta hanyar Sasanci.
A taron shi da Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a ranar Asabar da daddare, Buhari daya yi kira ga ƴan Takarar dasu zaɓi Ɗan Takarar Shugaban a tsakanin suz, yace zai tattauna da Masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar.
Yace “wannan shine karo na biyu a jere, kuma ina saran zan sake yin taro da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar.
Wannan sune matakan da ake ɗauka domin tabbatar da cewa haɗin kai da fahimtar Jam’iyyar an tabbatar dashi.
Comments 1