Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fara jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Sai dai kuma Buhari ya isa zauren majalisar ne da misalin karfe 11:00 na safe, kimanin sa’a daya bayan karfe 10:00 na safe.
KU KARANTA: Kotun Koli Ta Ɗage Shari’ar Daina Karbar Tsofaffin Kuɗi A Najeriya
Akwai sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugabar ma’aikatan tarayya Dr Folasade Yemi-Esan.
Kazalika Akwai kuma ministocin yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; Justice, Abubakar Malami; Kasafin Kudi da Tsarin Kasa; Zainab Ahmed, Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami; Babban Birnin Tarayya, Mohammed Bello da Ilimi, Adamu Adamu.
Sauran sun hada da ministocin harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Sadiya Farouq; Lafiya, Dr Osagie Ehanire; da kuma Karamin Ministan Noma, Mustapha Shehuri, Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa Clement Agba, da dai sauransu.
Mataimakin shugaban kasa Osinbajo baya halartar taron na ranar Laraba saboda yana kan wani aiki a jihar Legas.
Haka kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari bai halarci taron ba.
A wani labarin kuma: Matakin CBN Na Kin Karɓar Tsohon Kudi Tamkar Cin Fuska Ne Ga Kotun Koli – Lauyoyi
Wasu manyan lauyoyi biyu, sun ce bijirewa umarnin kotun koli da babban bankin Najeriya ya yi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Manyan Lauyoyin na mayar da martani ne kan kin bin umarnin Kotun Koli da CBN ya yi a makon jiya da ta hana shi aiwatar da wa’adin ranar 10 ga Fabrairu kan Tsofaffin kudi. DAILY POST ta rawaito.