Firaministan kasar Netherlands, Mark Rutte a ranar Talata ya ziyarci Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
Shugabannin biyu suka shiga wata tattaunawa ta musamman a cikin karamin dakin taron fadar shugaban kasa, inda ake sa ran za su cimma matsaya akan wasu jarjeniyoyi zuwa karshen zaman.
Jakadan Nijeriya a kasar Netherlands, Oji Ngofa ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya cewa wannan ziyarar za ta samar wa Nijeriya dama iri-iri musamman a fannin noma da kere-kere.
“Wannan ziyarar za ta bamu damar duba kyakkyawar alakarmu, kuma mu sake duba wasu yarjeniyoyin da zamu shiga. Wannan ziyarar lallai abin farin ciki ne matuka, ban taba ganin abu mafi alheri ga kasar nan ba kamar wannan ziyarar.
“Kasarsu na da tattalin arziki mai karfi, kuma su ne na biyu a duniya wajen noman abinci.
“Sun ci gaba sosai a fannin kirkire-kirkire da fasaha musamman a fagen noma da kasuwanci,” inji Ngofa.