By Abbas Yakubu Yaura
A yau Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu tsaffin shugabannin Najeriya.
Shugaban ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Villa dake Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar da kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Taron ya tattauna batutuwan da suka shafi muradun kasa da suka hada da yanayin tattalin arziki, rashin tsaro da kokarin gwamnati.
A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa ta karbi kudirin halatta kudin haram da kuma rigakafin ta’addanci.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar shugaban a zauren majalisar a ranar Alhamis.
Buhari ya ce bukatar amincewa da dokar ta kasance ne bisa tanadin sashe na 58(2) na kundin tsarin mulkin na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Ya koka da gazawar da ake samu a Najeriya’s na yaki da halatta kudin haramun da yaki da tallafin mulkin ta’addanci (AML/CFT).
Buhari ya yi gargadin cewa rashin amincewa da kudirin na iya haifar da bata sunan Najeriya daga hukumar kula da harkokin kudi ta FATF
Comments 1