By Ishaq Dabai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin guda uku na hukumar zabe mai zaman kanta INEC
An dai gudanar da bikin ne a takaice kafin fara gudanar da babban taron majalisar zartarwa ta tarayya FEC na mako a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wadanda aka rantsar sun hadar da Dr Baba Bila mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas, Farfesa Sani Adam, Arewa ta Tsakiya da Farfesa Abdullahi Abdu, mai wakiltar Arewa maso Yamma.
A halin yanzu Buhari yana jagorantar taron FEC na mako -mako a dakin taro na ofishin uwargidan shugaban kasa dake fadar sa.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya SGF, Mista Boss Mustapha, na cikin wadanda suka halacci taron.
Akwai kuma Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Babban Lauyan Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da kuma ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu.
Sauran sun hada da ministan kasafin kudi da tsare -tsare na kasa, Misis Zainab Ahmed, da na Ayyuka da Gidaje, Babtunde Fashola, da ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbeshola.
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan da sauran Ministoci da suka halarta.