Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar gyaran dokar zabe ta 2021, inda a yanzu ta zama doka.
An yi bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a cikin zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa a Abuja da misalin karfe 12:30 na ranar yau Juma’a.
Daga cikin wadanda suka halarci taron, yayin da shugaban kasar ke amincewa da kudirin ya hada da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mahmood Yakubu; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da sauran su.
Yarjejeniyar dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gamayyar kungiyoyin farar hula suka gudanar da zanga-zangar neman tilastawa shugaban kasar amincewa da Kudirin dokar da aka yi wa kwaskwarima.