Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da maido da tsofaffin takardun kudi na N200 a matsayin kudin da za a ci gaba da amfani da su. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa yan Najeriya jawabi da safiyar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu ajiye wa wani yanki shugaban kasa — Dattawan Arewa
“Na amince wa CBN cewa a bar tsohuwar takardar N200 tare da sabbin N200 na tsawon kwanaki 60 daga ranar 10 ga Fabrairu zuwa 10 ga Afrilu, lokacin da tsohuwar takardar N200 za ta daina aiki.
“Duk da haka duk tsofaffin takardun kudi na N500 da N1,000 suna nan jibge a CBN.
“Na kuma bukaci CBN da ya sa sabbin takardun kudi su wadaci ‘yan kasa a bankuna,” in ji Buhari
A wani labari kuma, Karanci Sabbin Kudi: Yan sanda Sun Kama Mutane 9 Da Su Bankawa Banki Wuta
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wasu mutane da aka bayyana a matsayin “matasa marasa kishin kasa/miyagu” biyo bayan tashe-tashen hankulan da ake samu kan karancin naira. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Matasa da dama ne a ranar Larabar da ta gabata, domin adawa da rashin samun sabbin takardun naira, suka kona bankuna da ababen hawa. Wasu kuma sun lalace a wani bangare.