Daga: Abbas Yakubu Yaura
A halin yanzu dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yana jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Taron majalisar tsaron ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya; Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwamacala: Kasashe 4 Da Mata Zasu Iya Auren Namiji Fiye Da Daya
Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Amao; da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Manjo Janar Samuel Adebayo, su ma sun halarci taron.
Sauran sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Usman Baba; Babban Darakta Janar na DSS, Yusuf Bichi; da kuma Darakta-Janar na hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.
A wani labarin kuma, Yanzu-yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Sanata Akpabio
Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta karba tare da buga sunan Godswill Akpabio, a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na mazabar Akwa Ibom ta arewa maso yamma a zaben shekara mai zuwa na 2023.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa INEC ta aikata ba bisa ka’ida ba saboda ta ki karba da kuma buga sunan Akpabio ko da APC ta aike mata da shi a matsayin dan takararta.