Akwai kwararan bututun iskar gas a kusa da unguwar Ikeja da ke Legas kuma an shawarci mazauna garin da ka da su kunna wuta a Yankin baki daya.
An gano yoyon iskar gas din ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Laraba Kuma, jami’ai daga Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NNPC) da hukumomin kashe gobara na tarayya da na Jiha na kan hanyarsu ta fara aikin gyarawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, bututun iskar gas dake Kai iskar zuwa masana’antu a yankin masana’antu na Ikeja ne ke yoyo.
Rundunar ‘yan sandan yankin Ikeja, ta killace yankin gabanin isowar masu gyaran bubutun.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Harbe Wasu Jami’an Yan sanda a Jihar Rivers
Ko’odinetan Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na shiyyar Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, a wani sako da ya aike ta WhatsApp, ya shawarci jama’a da su yi iya kokarinsu don kaucewa wannan wuri.
Ya Kuma kara cewa, “Mazauna kusa da yankunan Computer Village/Underbridge, Awolowo Way da Oba Akran axis, Titin Onifowose, Titin Medical , kada su bude shaguna ko Bude shaguna, saboda dalilai na tsaro.
“Sakamakon tashin hankali da aka samu na nuni da kwararar bututun iskar gas a kusa da wadannan wuraren. Mu dauki tsauraran matakan tsaro,” a cewar shi.