Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da mutuwar karin mutum uku sakamakon cutar Korona.
Kwamishinan Lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar. A cewarsa, ya zuwa yanzu jumullar mutanen da suka mutu sun kai 13.
Sannan ya tabbatar da cewa an samu sabbin masu dauke da cutar korona guda 32, yanzu ke nan adadin masu fama da cutar a jihar ya kai 286.