Dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola ya rasu.
DAILY POST ta tattaro cewa Popoola ya mutu ne da sanyin safiyar yau Laraba.
Dan majalisar dai yana wakiltar mazabar Ibadan ta kudu maso gabas II a majalisar dokokin jihar Oyo.
Wakilin majiyar jaridar Dimokiradiyya ya ruwaito cewa dan majalisar ya rasu ne a asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan.
An zabi dan majalisar ne a shekarar 2019 domin wakiltar yankin a jam’iyyar PDP.
Rahotanni sun nuna cewa dan majalisar ya rasu ne bayan ya yi fama da cutar koda.
Ya rasu yana da shekaru 46 a duniya.
Kafin rasuwarsa Popoola shi ne Shugaban, Kwamitin Majalisa kan Al’amuran Kananan Hukumomi da Sarautun gargajiya.
Oyekunle Oyetunji, mai baiwa kakakin majalisar dokokin jihar shawara kan harkokin yada labarai, Adebo Ogundoyin, ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar a safiyar yau Laraba.
Ya ce, “Na’am. An tabbatar”.
A wani labarin kuma na daban.
Faraministan Sri Lanka ya ayyana dokar ta baci a dukkan fadin kasar
Firaminista ya ayyana dokar ta-baci a duk fadin Sri Lanka kuma an sanya dokar ta-baci a lardin yammacin kasar, in ji mai magana da yawun ofishin Firaminista.
Wannan na uwa ne yayin da Dubban masu zanga-zangar ke kan hanyarsu ta zuwa ofishin firaministan da ke kan titin Flower – kimanin mintuna 20 daga babban wurin zanga-zangar na Galle Face Green.
Firaminista Ranil Wickremesinghe ya ce zai sauka daga mulki da zarar an kafa gwamnatin rikon kwarya ta jam’iyyarsa bayan ficewar Mista Rajapaksa.
Amma ‘yan kasar Sri Lanka da yawa suna son ya bar mulkin nan take.
Wannan saboda da zarar Mista Rajapaksa ya tashi, a karkashin tsarin mulkin Sri Lanka, Mr Wickremesinghe zai zama shugaban riko na tsawon kwanaki 30 kai tsaye.
Buddhi Prabodha Karunatne mai zanga-zangar ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Idan ba mu ji murabus din shugaban kasa da firaministan kasar da maraice ba, to lallai ne mu dawo mu karbe majalisar dokoki ko kuma wani ginin gwamnati.”
“Muna adawa da gwamnatin Gota-Ranil. Dukansu dole ne su tafi.” Inji shi.