Wani Dan majalissar dokokin tarayya dake wakiltar mazabar Akure ta Kudu da Akure ta Arewa, Mai suna Mr Adebayo Omolage Wanda akafi sani da “Expensive” ya mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Omolafe Dan majalissa ne daya lashe zabe a inuwar jam’iyar PDP, ya rasu ne da musalin karfe biyu na safiyar yau Litinin, a gidan shi dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jami’in yada labarai na jam’iyar adawa ta PDP Kennedy Peretei ne ya tabbatar wa da Jaridar Dimokuradiyya rasu war dan majalissar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Auren Zahra Diamond, da cire Ummi Rahab, menene makomar Farin Wata?
Ya ce, “Kwarai Dan majalissar ya mutu ne a garin Abuja da safiyar yau Litinin, Kuma muna daf da sakin wata sanarwa akan hakan” inji shi.
An zabi Omolafe a zaben shekarar 2019, a karkashin inuwar jam’iyar PDP domin ya kwakillci yankin Akure ta Arewa, da kuma ta Kudu, a majalissar dokokinta Tarayya, bayan ya kwashe tsawon lokaci, ya na neman kujerar, tun daga lokacin da ya ke kan kujerar karamar hukumar Akure ta Kudu a shekarar 2009.
Akwai Karin bayani….
A wani labarin Kuma na daban.
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah, da Babbar Murya tayi Allah wadai da Kwanton bauna tare da Kashe Matafiya Musulmai da akayi, a hanyar Rukuba ta Jos.
Wasu Yan ta’adda a ranar Asabar da ake kyautata zaton mazauna yankunan ne, suka farmaki motoci dauke da matafiya Musulmai, tare da Kashe mutane 22, gami da raunata mutane da dama.
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana hakan a cikin sanarwa da Sakataren Kungiyar na Kasa Baba Othman Ngelzarma ya fitar, a ranar Lahadi a Jos, inda yace har yanzu ba’a San inda wasu daga cikin Matafiyan suke ba.
“Lamarin ya faru da Misalin Karfe 10:00 na safiyar jiya, inda aka raunata matafiyan da dama, a yayinda har yanzu mutane 40 ba’a San inda suke ba.
“Matafiyan sun taho ne a jerin gwano na motoci, a yayinda Yan ta’addan suka kai masu hari.
“Muna Kira ga Hukumomin tsaro dasuyi gaggawar gano wadanda suka aikata lamarin, tare da gabatar dasu a gaban kuliya domin girbar abinda suka aikata,”inji shi.
Ngelzarma ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa Yan uwansu da Kuma wadanda suka ji rauni.
Yace dole wannan kisan na hauka da rashin hankali ya tsaya, a daina gudanar dashi.