Tijjani Ibrahim Gaya dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC a gundumar Jigawa ta Kudu maso Yamma ya rasu.
Ya rasu ne a wani asibitin kasar Sin a ranar Asabar.
An ce an kwantar da shi a wani asibitin Abuja sakamakon ciwon huhu amma an garzaya da shi kasar China domin ci gaba da kula da lafiyarsa a lokacin da yanayinsa jikin nasa tabarbare.
Marigayi Gaya ya lashe tikitin takarar Sanata na APC na shiyyar sa watanni uku da suka gabata.
A halin da ake ciki, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya bayyana rasuwar Gaya a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, ga al’ummar musulmi baki daya.
Najeriya Bata Taɓa Dacen Shugaba Irin Buhari ba Tun Daga 1999 – Inji Ministan Buhari
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Habibu Nuhu Kila, gwamnan ya jajantawa iyalan mamacin.
“Gwamnan ya ce rasuwar Honorabul Tijjani Ibrahim Gaya babban rashi ne ba ga iyalansa kadai ba har ma da al’ummar musulmi.”
“Ya bayyana marigayi Alhaji Tijjani Ibrahim Kiyawa a matsayin dan siyasa mai kishin kasa kuma rikon amana wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban siyasar kasar nan.
“Gwamna Badaru ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da Ya jikansa da rahama, tare da iyalansa da karfin juriyar rashin,” in ji sanarwar.
Marigayin dan siyasar ya wakilci mazabar Dutse/Kiyawa tarayya a majalisar wakilai tsakanin shwkarar 2011 zuwa shekarar 2015.