Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar Joseph Egbunike, ya rasu.
Cikakkun bayanai game da mutuwarsa sun kasance zayyane a lokacin da wannan rahoto ya fito.
Marigayin ya jagoranci kwamitin da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya kafa domin gudanar da bincike a kan zargin da FBI ke yi wa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari.
Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta ce dan damfarar Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi ya aika wasu kudade ga Kyari, zargin da dan sandan ya musanta.
Bayan watanni, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta gurfanar da Kyari a gaban kotu bisa laifin cinikin hodar iblis. Yanzu haka dai Kyari yana tsare.