Ana zaman dar -dar a garin Bida da ke jihar Niger, yayin da direbobin tanka suka toshe dukannin manyan hanyoyin shiga garin, tare da hana masu ababen hawa shige da fice yankin baki daya.
Rahotanni sun nuna cewa, Duk manyan hanyoyin da ke cikin garin direbobin tankan sun toshe su, domin nuna rashin jin dadin su ga mummunan lalacewar da hanyoyin da ke jihar suka yi, musammanma hanyar da ta taso daga Bida zuwa Lapai da kuma Lambata.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta bayyana cewar,Fasinjojin da ke tafiya zuwa jihohi daban-daban na bangaren yankin Gabashin kasar nan, da Kudu, da Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas, da kuma Arewa ta Tsakiya yanzu sun yi cirko-cirko a yankin na garin Bida.
Hakan Kuma ya Sanya, Bata gari a yankin suna karban Naira 20 zuwa 50, kafin su bar Masu amfani da Babura haya, amfani da kananan hanyoyin da direbobin tankar ba su toshe ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda El’Rufa’i ya sauya Tattalin Arzikin Kaduna cikin Kankanin lokaci
Lamarin dai ya fi munana musamman a yankin Esso na Garin Bida, sakamakon yadda ababen hawa suka tsaya.
Kazalika Mazauna garin sun yi kira ga gwamnan jihar Abubakar Sani Bello, da ya gaggauta shiga tsakani kafin lamarin ya munana.
Comments 1