Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta cafke kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo.
Kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, ne ya tabbatar da hakan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya’yan Jam’iyun PDP, SDP, NNPP Sama Da 500, Sun Sauya Sheka Zuwa APC A Jigawa
An kama shi ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Majiyoyi sun shaida wa wakilin sashen kula da harkokin shari’a na gidan Talabijin na Channels, Shola Soyele, cewa jami’an hukumar EFCC sun dauke shi ne domin amsa tambayoyin da suka shafi laifukan badakalar kudi.
Shugabancin Hukumar dai sun tsare shi ne akan kan wani bincike, amma ana sa ran nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa kan batun.
Sai dai wata majiya a cikin Hukumar ta amince da cewa hukumar EFCC ta gayyaci kakakin majalisar jihar Ogun sau da dama amma ya kasa amsa gayyatar ta.
An dai kai Oluomo ofishin EFCC na Legas don ci gaba da yi masa tambayoyi.
A WANI LABARIN KUMA: Na Siyar da Motar Maigidana Don Na Gudu Na Bar Najeriya —Wanda Ake Zargi
An kama wani matashi dan shekara 21 mai suna Temple Samuel da ‘yan sanda suka kama shi a jihar Legas, ya bayyana cewa ya siyar da Motar ubangidansa mai suna Lexus 330 ne don biyan kudin tafiyarsa zuwa kasar waje.
Wanda ake zargin tare da wasu mutane uku da aka kama a unguwar Ogba da ke jihar, ya ce, “ Na yi Niyyar guduwa da motar oga na be, domin in sayar, kuma inyi amfani da abin da aka samu wajen tafiyata zuwa kasashen waje. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito