Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC, ta kama tsohon gwamnan jihar Abia Theodore Orji, a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa-da-kasa na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja.
Tsohon gwamnan dake daya daga cikin komar Hukumar EFCC, an kama shi ne da musalin karfe goma na safiyar yau Alhamis, inda kuma hukumar ta kai shi shelwatarta dake yankin Jabi na garin Abuja, domin amsa wasu tambayoyi.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, hukumar EFCC ta kama Orji ne tare da Dan shi Chinedu, Wanda shi ne kakakin majalissar Dokokin jihar Abia.
Sanata Orji da Dan sa Chinedu da kuma Ogbonna, na cikin komar Hukumar EFCC bisa zargin madakala da kudaden al’uma da suka kai Naira Billiyan 551.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalara: Mutum 1,665 sun kamu a Kaduna, cikin watanni 5
Kazalika ana zargin tsoton gwamnan ne, da sama da fadi da naira milliyan dari biyar a ko wani wata, har na tsawon watanni 8, lokacin mulkin shi na Gwamnan jihar Abia, a shekarar 2007 zuwa 2015.
Sauran madakalar sun hada da zargin karkatar da kudaden Asusun kula da Muhalli, da kudaden sharin Sure-P da suka kai Naira Billiyan 2.
Kuma daka tuntumi Mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama tsohon gwamnan.