Tsohon ministan harkokin waje na Nijeriya, Farfesa Ibrahim Gambari, ya maye gurbin Marigayi Abba Kyari, inda ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya.
Farfesa Gambari ya maye gurbin Abba Kyari ne bayan da cutar Korona ta kashe Abba Kyari a watan da ta gabata. Inda kujerar ta zauna ba kowa.
Majiyarmu ta Jaridar THISDAY ta ce Gambari, ya rike mukamin ministan harkokin waje a shekarar 1980 da na mulkin soja na Buhari, ya gana da shugaba Buhari da misalin karfe 8 na safiyar yau Talata a fadar gwamnati dake Abuja.
Zai fara aiki ne daga ranar Laraba.