Yanzu-Yanzu: Fasinjan Jirgin Azman Sun yi Cirko-Cirko na tsawon awanni 24 a Kano
Matafiya na Jirgin Azman sun yi zama na tsawon awanni 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Malam Aminu Kano dake Kano.
Wasu Matafiyan sai dai su ƙara kwana a cikin Filin Jirgin, domin basu da masaniya kan canja masu lokaci sai zuwa yammacin wannan rana.
Da yawa daga cikin Matafiyan, da zasu je Abuja zuwa Lagos sun koka kan yadda ya kamata ace sun tashi daga Karfe 4 na ranar Asabar, amma an canja masu lokaci da misalin ƙarfe 8 na dare.
“Ina nan tun jiya, kuma nuna saran tashi daga ƙarfe 4 amma mutane basa nan ballantana su gaya mana wani abu. Sai ƙarfe 8 muka samu masaniya cewa an canjawa jirgin lokacin tashi zuwa yau (Lahadi). Wasu sun kwana anan. Wannan abun damuwa ne”, Inji Jamilu Rabiu wani daga cikin Matafiyan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗumi-ɗuminsa: NFF ta naɗa José Peseiro a matsayin Shugaban Masu Horas da Super Eagles
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa Jirgin yana fama da matsala da masu Sayar da Man Jirage.
Ɗaya daga cikin Ma’aikatan Jirgin yace da yawa daga cikin Matafiyan da suka haɗa da Mata da Ƙananan Yara ya zaman masu abu mai wahala su koma inda suka fito, ko kuma kama Otel domin su kwanta.
Ɗaya daga cikin Ma’aikatan Jirgin Azman yace hakan ya faru a dalilin matsalar da ta faru ga Jirgin, yana mai basu tabbacin tashi da misalin ƙarfe 6:30 na yamma (a ranar Lahadi).