Wasu rukunin shagunan zamani da ake kira da NEXT, dake a yankin Kado, na Babban Birnin Tarayya Abuja, gobara ta tashi a wajen.
Har yanzu babu cikakken rahoton tashin gobarar, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Supermarket ɗin na ɗaya daga cikin manyan Shagunan zamani dake a Babban Birnin Tarayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ba Ya Goyon Bayan Wani Tsagi A Shugabancin APC Kano
A wani Labarin kuma
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya musanta amincewa da wani bangare na shugabancin jam’iyyar APC a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.
“Fadar shugaban kasa na son yin tir da furucin da daya daga cikin bangarorin jam’iyyar (APC) a jihar Kano ya yi a bainar jama’a, cewa sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari,” in ji sanarwar.
”Wannan ba gaskiya bane a fili. Wannan ba zai iya faruwa ba lokacin da al’amura ke jiran hukunci daga kotuna”.
‘’Don a fayyace wannan, Shugaba Buhari bai amince da wani bangare ba’’.
A cewar sanarwar, goyon bayan sa ga jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya ce, hadin kai da karfi, ba na kowane bangare ba.