An sauke kwamishinan harkokin addini na jihar Kano, Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) daga mukaminsa.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba, ya ce antsige shi cikin gaggawa.
KARANTA KUMA Gwamnatin Kano Ta Yi Alkawarin Miliyan 10 Ga Wata Islamiyya
Ya ce korar kwamishinan kuma dan majalisar zartarwa ta jihar ya biyo bayan halin rashin da’a ne a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami, da kuma kalamai marasa kangado.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, an kuma same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa ne a matsayin sana’a, har ma yana rage ranakun aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, inda ya kebe ranakun Laraba da Juma’a.
Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.
Ya kara da cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar dokokin jihar sunan Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano a matsayin wanda zai maye gurbinsa domin tantancewa da nada a matsayin sabon kwamishina.
sanarwar ta kara da cewa, Gwamnan ya yi fatan korar kwamishinan ta zamar masa alheri.
A Wani Labarin Kuma Mazauna Maiduguri Sun Wayi Gari Da Ganin Gawar Mutum A Magudanar Ruwa
Wani jami’in rundunar ‘Civilian Joint Task Force’ (CJTF) ya dauke gawar wani matashi da aka jefar a magudanar ruwa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Wakilinmu da ya ziyarci wurin a safiyar ranar Asabar, ya ga wani matashi da jini an lullube shi, aka jefar a kusa da na’urar taranfoma da ke Old GRA, kusa da tsohuwar makarantar International da ke kan titin Damboa, a Maiduguri.