Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun ta ce za ta gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar Osun a ranar 15 ga Oktoba, na shekarar 2022.
Shugaban Hukumar, Otunba Olusegun Oladuntan ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Osogbo ranar Litinin din nan.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/apc-ba-ta-da-%c6%b4an-takarar-sanata-a-yobe-da-akwa-ibom-inec/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Oladuntan ya ce a yanzu hukumar tana aiki kan sabuwar dokar zabe ta 2022 da majalisar jihar ta amince da ita a jihar ta Osun.
Ya ce hukumar ta kuma gudanar da taron tattaunawa da jam’iyyun siyasa domin yi musu bayani kan tsare-tsaren zaben.
Insighit links/Nigeriantracker