Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya rusa majalisar zartarwa ta jihar,Punch ta rawaito.
Wike ya sanar da rushewar ne bayan wani taron zartarwa na musamman a gidan gwamnati da ke Fatakwal a yammacin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN: Kwanaki 5 Yabar Ofis: Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Asusun Bunkasa Noma Na Kasa
Tun da farko dai kwamishinonin sun yaba wa gwamnan bisa irin nasarorin da ya samu a jihar.
Mai taimaka wa Gwamnan kan harkokin yada labarai Kelvin Ebiri ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho.
A wani labarin kuma, Ban San Komai Ba Game Da Ma’aikatar Ilmi Sanda Aka Nada Ni Minista – Adamu
Ministan Ilmi Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa shi ba shi da masaniya a fannin ilimi lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi ministan ilimi a shekarar 2015.
Malam Adamu, wanda shi ne minista mafi dadewa a kan karagar mulki, ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da aka yi da jami’ai da shugabannin hukumomin ma’aikatar a ranar Alhamis din nan.
Ya ce an tilasta masa yin amfani da hikima ta hanyar nada wasu farfesoshi na ilimi da sauran nagartattun hannuwa, tare da taimakon jami’an ma’aikatar ilimi ta tarayya don ba shi damar farawa da samun ci gaba.
Ministan ya yaba wa Shugaban kasar da ya ga ya cancanta kuma ya amince masa wajen dora masa irin wannan nauyi.