Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci mazauna jihar Kaduna da su zauna cikin shirin rufe ayyukan sadarwa, yayin da jami’an tsaro ke shirin kaddamar da farmaki kan ‘yan bindiga da ke fakewa a wasu kananan hukumomin jihar.
El-Rufa’i ya Kuma ce, rufewar ba zai shafi jihar baki daya ba, Amma da yuwuwar lamarin ya shafi wasu kananan hukumomin da ke makwaftaka da jihar Zamfara da Katsina inda ake ci gaba da kai farmakin soji.
Da yake magana yayin tattaunawa da zababbun gidajen rediyo a Kaduna a daren jiya Talata, Gwamna El-Rufai ya ce: “Sojoji da sauran hukumomin tsaro sun shawarce mu da mu rufe ayyukan sadarwa a wasu kananan hukumomi, amma muna jiran hukumomin tsaro su fadamana takamaiman yankunan da abun zai shafa da kuma lokacin da za’a katse sadarwa”
“Amma ina son mutanen jihar Kaduna su sani cewa, idan sun ba mu bayanai ko gobe ne, wato yau Laraba, to za mu rufe goben.” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda zata dauki sabbin jami’ai 20,000
El-Rufai, wanda yai magana da harshen Hausa, ya ce saboda rufe ayyukan sadarwa a jihohin Zamfara da Katsina, rahoton ya nuna cewa, wasu ‘yan bindiga sun tsallako zuwa kananan hukumomin dake makwabta da jihohin a jihar Kaduna, don yin kiran waya da neman kudin fansa.
“Babu shakka ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka, sun dogara da hanyar sadarwa, tare da masu ba su bayanan sirri, da kuma dangin wadanda aka sace, don neman kudin fansa,” acewar shi.
Gwamnan ya kuma cigaba da cewa, tuni ya rubutawa gwamnatin tarayya wasikar rufewar, wanda ya ce tuni kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ita.
“Ba zan ambaci kananan hukumomin da abin zai shafa ba, amma kananan hukumomin da ‘yan bindiga ke azabtar da su kullum sun san kansu.”
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa,kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kajuru da Kachia sune suka fuskantan yawan hare -haren yan bindiga a jihar Kaduna.