Gwamnatin tarayya ta tsaida matsayar haramta wa duk wani wanda ba dan Najeriya sa kuma yan Najeriya shigowa Kasar nan daga Ƙasashen Indiya da Turkiya sa Brazil.
Wannan mataki na zuwa ne a wani yunkurin na dakile bazuwar cutar Korona izuwa kasar, ganin yadda cutar take kara kunno kai a ƙasashen duniya kamar yadda kwamitin fadar shugaban kasa kan cutar korona ta bayyana.
Shugaban Kwamitin Mista Boss Mustapha cikin wata sanarwa ya ce haramcin zai fara aiki ne daga ranar talata mai zuwa, kana daga bisani bayan makonni hudu a ga mai za a sake yi.
A cewar Sanarwar kuma duk wasu wadanda suka shigo kasar daga wasu ƙasashe, to lallai za su zauna a dakin duhu har tsawon mako guda gabannin daukar matakin barinsu shiga al’umma.