Gwamnatin Tarayya ta hannun Ministan Kwadago Chris Ngige, na shirin ganawa da Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i a yau Litinin, 11 ga Afrilun Shekarar 2022, inji rahoton Jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Taron wanda zai fara da karfe 5 na yamma zai samu halartar wakilan gwamnatin tarayya da kuma kungiyar ASUU.
Daraktar yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya Patience Onuobia, a cikin sanarwar taron da ta aikewa ‘yan jarida a ranar Litinin, ta ce Ngige ne zai jagoranci taron da kan sa.
“Ministan Kwadago da Samar da ayyukan yi na kasa Dr. Chris Ngige, zai gana da kungiyar malaman jami’o’i a yau da karfe 5 na yamma,” inji sanarwar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa kungiyar ASUU ta shiga kwana 56 a yau Litinin da tsunduma cikin Yajin aiki.
Tun da fari, A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, shekarar 2022, ASUU ta sanar da yajin aikin gargadi na tsawon mako hudu, biyo bayan gazawar kungiyar da gwamnatin tarayya wajen cimma matsaya kan bukatun malaman jami’o’in.
Wasu daga cikin bukatun ASUU sun hada da sakin kudaden farfado da jami’o’i, sake tattaunawa kan yarjejeniyar gwamnatin Tarayya da kungiyar ta ASUU na shekarar 2009, sakin kudaden alawus-alawus ga malaman jami’o’i, da amfani da tsarin biyan UTAS na biyan albashi da alawus-alawus na malaman jami’o’i, a maimakon IPPIS
Bayan karewar makonni hudun farko na yajin aikin gargadi, kungiyar ta riga ta ayyana karin makonni takwas tana mai cewa tana baiwa gwamnati karin lokaci domin biyan bukatunta.